8 Maris 2022 - 15:58
An Kasa Cimma Matsaya A Tattaunawar Sulhu Da Aka yi Zagaye Na 3 Tsakanin Rasha Da Ukrain

Rahotanni sun bayyana cewa An kammala tattaunawar sulhu tsakanin kasashen Rasha da Ukrani batare da kulla wani abin azo a gani ba, sai dai jami’an gwamantin kasar Ukrain sun nuna cewa an samu canji kadan game da hanyoyin da za’a bi wajen kare fararen hula.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Zagayen farko na tattaunawar an yi ta ne a birnin Gomle na kasar Belarus a ranar 28 ga watan Fabareru , sai na biyu kuma an shi ya ne a ranar 3 ga watan maris a garin Brest Bloer dake kusa da iyaka,

Sai dai ya zuwa yanzu bbau wani ci gaba da aka samu , a nasa bangaren mai shiga tsakani na kasar Ukrain a tattaunawar ya wallafa a shafinsa na twiter bayan tattaunawar cewa akwai wani ci gaba kadan da aka samu day a shafi kare rayukan fararen hula, sai dai bangarorin biyu za su ci gaba da tattaunawar game da batu tsagaita bude wuta.

A nasa bangaren mai shiga tsakani na kasa Rasha Viladmir Madinsky ya fadi cewa yana fatan batun bude hanyoyin kare fararen hula a kasar Ukrain zai fara aiki a yau talata, sai dai babu abin da aka cimma a bangaren siyasa, sai dai akwai kyakkyawar tattaunawar ta gaba za ta haifar dad a mai ido.

342/